Site icon Muryar 'Yanci

2023: Mata Da Matasa Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mata da matasa da dama a fadin jihohin arewa 19, a ranar Juma’a, sun yi tururuwa a Abuja domin marawa jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu baya.

Sun nemi a tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar mai mulki a zaben shugaban kasa mai zuwa, domin ?orawa daga inda Buhari ya tsaya.

Har ila yau, sun bayyana cewa Tinubu ne mutum daya tilo da ya cancanta kuma zai iya a cikin dukkanin masu takarar da suka ayyana kudirinsu na son daidaita tattalin arzikin kasar.

Karkashin jagorancin Yakubu Dauda, sun bayyana cewa matasa da matan APC a jihohin arewa 19 sun kasance dumu-dumu a harkokin jam’iyyar ta hanyoyi daban-daban wanda ya karfafa jam’iyyar a zukatan mutane.

“Muna fatan sanar da shugaban kasa cewa muna ta tattarawa jam’iyyar magoya baya a dukkan matakai a fadin jihohin arewa 19 yayin da ake shirye-shiryen zaben 2023.

“Irin karbuwar da Tinubu ya samu a tsakanin talakawa abu ne mai ban mamaki za a iya tunanin cewa daga yankin arewa ya fito. “A matsayinmu na gagarumar kungiya a cikin matasa da mata a jihohin arewa 19, ciki harda babbar birnin tarayya, muna iya fadi ba tare da tsoro ba cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu karbuwa sosai a matsayin babban dan takarar jam’iyyarmu mai albarka a babban zaben 2023 mai zuwa.”

Exit mobile version