Gwamna Nasiru Ahmed El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana cewa yana ji a ransa wannan karon Mace ce za ta zama Gwamniya a Jihar Kaduna a za?e mai zuwa kamar yadda jaridar mikiya ta ruwaito.
El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin amsa tambayoyi na musamman daga ?an Jaridu a Jihar Kaduna. Ya ce, akwai yiwuwa da kaso 50% wanda yake ji a ransa cewa Mace zata zama Gwannan Jihar ta Kaduna.
Gwamman wanda a halin yanzu yake jagorantar Jihar tare da taimakon mataimakiyarsa wato Dr Hadiza Balarabe, ya ?ara da cewa Gwamnatin ta Jihar Kaduna, za ta cigaba da baiwa mata damarmaki wajen taka irin ta su rawar a gwamnatance.
Kamar yanda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito, El-Rufai, ya kuma yi kira na musamman ga sauran alummar Nigeria akan su baiwa mata da matasa dama ta fannin shugabanci domin hakan zai kawo cigaban ?asa.
A ?arshe, yayi adduar neman taimako daga Allah, akan Ya za?awa alummar Kaduna mutum nagari wanda zai kyautata rayuwar alumma, tare da gyara kurakuran da yayi domin cigaban Jihar Kaduna.

