Site icon Muryar 'Yanci

2023: Ina Da Yakinin Zama Shugaban Kasa – Ministan Kwadago

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Kwadago da Ayyuka, Sanata Chris Ngige, ya ce Ubangiji ya masa magana game da niyyarsa na takarar shugaban kasa kuma zai kaddamar da takarar ranar Talata.

An ruwaito cewa Ngige ya furta hakan ne a ranar Asabar da yamma a lokaci da mambobin jam’iyyar APC suka tarbe shi a wata mahada tsakanin Jihar Anambra da Enugu.

Da ya ke yi wa dandazon mutanen jawabi, wanda tunda farko suka bukaci ya fito takarar, Ngige ya ce ya tuntubi mutane, kuma ya yi addu’a sannan Ubangiji ya amsa shi.

“Ina son in tabbatar muku lokacin ‘azumin lent’ ta kare daren jiya, kuma a lokacin, mun kusanci Ubangiji. Mun yi addu’o’i da azumi. Munyi magana da Ubangiji da mala’ikunsa kuma Ubangiji ya mana magana.

Ubangiji ya min magana. Ina son tabbatarwa mutane ba zan basu kunya ba. Zan muku magana a irin harshen da kuke fahimta,” in ji shi.

A daina kwatanta ni da Peter Obi da Willie Obiano, wata 34 kadai na yi a matsayin gwamnan Jihar Anambra cikin watanni 34, na yi ayyukan da wasu ba su iya yi ba cikin shekaru takwas a ofis.

Exit mobile version