Kungiyar APC Political Alliance (APA), ta yi gargadin cewa rigingimun siyasa a jamiyyar APC reshen jihar Kaduna wanda suke zargin gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na nuna son zuciya wurin tafiyar da mulkin adalci a matsayin sa na shugaba ba mulkin kama karya ba wanda hakan zai sa APC ta rasa kujerar mulkin jihar Kaduna ga jamiyyun adawa a zaben 2023 dake zuwa.
Kungiyar wacce ta kunshi dattawan mashahuran mutane, mata, matasa, da shugabannin masanaantu yayan jamiyyar APC ne kuma masu goyon bayan jamiyyar APC, ta ce matakin da Gwamna El-Rufai ya dauka na tilasta wa alummar jihar Kaduna ‘dan takarar da yakeson daurawa a matsayin magajinsa, zai raba kan jamiyyar. , kuma hakan zai sa jamiyyar ta yi asarar mulki a zaben 2023.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, kakakin kungiyar, Alhaji Shehu Abdullahi Mustapha, ya ce Gwamna a yan watannin nan yana tursasa shugabannin jamiyyar APC na jihar su nada dan takara.
Daga cikin wadanda Gwamna El-Rufia ya yi hasashe akwai Sanata kuma daya daga cikin kwamishinonin sa, matakin da kungiyar ta ce ba ta amince da shi a wajen mafi yawan yayan jamiyyar da shugabannin jamiyyar a fadin jihar da sauran jamaa ba.
Alhaji Shehu ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabannin jamiyyar APC na kasa da su kira Gwamna El-Rufai domin ya ceto jamiyyar daga rugujewa a jihar Kaduna.
Idan har anaso jamiyyar ta samu nasara a zaben 2023, ya zama wajibi shugaban kasa da sauran masu fada aji du tilasta wa Gwamna El-Rufai ya bar dan takara mafi farin jini da mafi yawan yayan jamiyyar da wakilai suka zaba ya fito. a matsayin dan takarar gwamna ba son zuciyar sa ba.” Inji Alh Shehu Abdullahi

