Site icon Muryar 'Yanci

2023: Bamu Bukatar Tsoho A Shugabancin Kasa – Matasan Najeriya

Kungiyar Matasan tarayyar Najeriya ta bayyana cewar ko ka?an baza su amince da takarar tsoho a kakar za?e dake tafe ta shekarar 2023 ba.

Shugaban kungiyar Matasan Najeriya Alhaji Abdullahi Abubakar Wali ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da yayi da wakilinmu a gidansa dake garin Kaduna.

Shugaban Matasan ya ?ara da cewar tsofaffi sun yi tasu rawar anga kamun ludayinsu wanda ke tattare da koma baya da tawaya, a halin da ake ciki yanzu lokaci ya yi da ya kamata wadannan tsofaffi su kau su ba matasa dama domin ciyar da ?asa gaba.

Matasan sun koka gami da nuna damuwarsu dangane da aniyar da tsohon gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu ya nuna na burin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023 da i?irarin ?orawa daga inda Buhari ya tsaya.

“Ba za mu ta?a goyon baya ko za?en Tinubu a shugabancin ?asa ba, saboda da dalilan tsufa da rashin lafiya, kuma muna kira ga Buhari da ya kame akan batun goya wa wani Mutum baya a babban zabe dake tafe”.

Dangane da halin ta?ar?arewar tsaro a Jihar Zamfara kuwa, Abdullahi Abubakar Wali wanda ?an asalin jihar Zamfara ne ya koka da yadda wasu manya a Jihar suke nuna halin ko in kula akan tsaron jihar, inda ya koka akan yadda babban masanin tsaron ?asa kuma jigo a Jihar Janar Ali Gusau ya yi shakulatin ?angaro da harkar tsaro a jihar.

Abubakar Wali ya shawarci manyan jihar ta Zamfara da yin koyi da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Dalhatu Bafarawa, wanda ya fito ya kalubalanci Gwamnatin Tarayya akan tsaro a jihar Sokoto, wanda maganar tashi tayi tasiri matuka.

Exit mobile version