Gamayyar kungiyoyin matasan arewa guda arbain da biyu (42) a karkashin inuwar kungiyar shugabannin matasan Arewa (NYLF) sun bayyana bukatar gwamnonin kudu na neman mika shugabancin kasa ga kudu a 2023 a matsayin rashin tunani, cin fuska, da kuma tsokana.
Shugaban kungiyar ta NYLF na kasa, Eliot Afiyo, wanda ya bayyana matsayin kungiyoyin a taron manema labarai a Yola, jihar Adamawa, ya ce gwamnonin kudu sun fallasa rashin gogewarsu da yarintarsu a siyasa da irin wadannan bukatun.
Matasan na Arewa na martani ne ga bu?atar gwamnonin kudu na baya-bayan nan inda suka gindaya sharadin cewa dole ne mulki ya koma kudanci a shekarar 2023, Afiyo ya ci gaba da cewa sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnonin kudu ba su da kwarewar siyasa da tsari.
“Mun dauki wannan furucin a matsayin mai tayar da hankali, rashin tunani, cin fuska, kalubale da kuma ayyana yakin siyasa wanda dole ne a ba shi cikakken tunani da aiki.”

