?ungiyar dattawan arewacin Najeriya ta ce babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta za?en wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin ?asar a zaben 2023.
?ungiyar ta mayar da martani ne ga matakin da ?ungiyar gwamnonin kudancin Najeriya da wasu ?ungiyoyi suka ?auka cewa lokaci ya yi da mulki zai koma bangarensu.
Kakakin kungiyar dattawan na arewa Dr Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa arewa tana da yawan masu zabe, don haka “yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana.”
A wani taron da gwamnonin kudancin Najeriya suka gudanar a watan Yuli sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na kar?a-kar?a daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ?asa da za a za?a a 2023 ya fito daga yankin kudancin ?asar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.
Kasancewar Najeriya mai bambancin ka?ilu da addinai, bisa al’ada jam’iyyun siyasa kan yanke shawarar yin kar?a-kar?a tsakanin yankin arewaci da kudanci. Kuma mutanen yankin kudanci na ganin yanzu lokacinsu ne, kasancewar yanzu shugaban da ke mulki ya fito ne daga yankin arewaci.
Sai dai kuma ?ungiyar dattawan arewa mai tun?aho da yawan jama’a a Najeriya ta ce ana nuna wa yankin yatsa da maganganu masu zafi cewar ko da tsiya ko da arziki sai mulki ya koma kudu.
“Idan ?an kudu na kwa?ayin a jefa masu kuri’a, ba zagi za su yi ba, ko suce a yi ko a mutu – ba kuma irin wannan izgili zai sa mu ji tsoro mu ce a zabi ?an kudu ba.
“Ba mu ce ba mu son ?an kudu shugaban kasa ba, amma irin barazana da bada tsoro shi ne ba za mu yarda da shi ba,” in ji Dr Hakeem Baba Ahmed.
Ya ?ara da cewa mulkin dimokuradiya ake yi, ko da yan siyasa sun je sun yi yarjejeniya, mutane ne za su jefa kuri’a, kuma mutanen arewa suna da za?i ko su za?i ?an kudu ko ?an arewa.
“Huruminmu ne kan wanda za mu za?a, ba na jam’iyyu ba, aikinsu kawai su tsayar da ?an takara – amma su sani akwai alkiblar da mutanen arewa suka sa a gaba,”
Ya kuma ce yankin arewa ba ruwansa da ra’ayin manyan jam’iyyun siyasa APC da PDP. “Abin da yake da amfani shi ne muna tuna masu duk abin da za su yi ko su kitsa – idan arewa ta ga dama ?an arewa za ta za?a, ba wani wanda zai tafi ya shirya ya zo ya ce wa yan arewa su zabi dan kudu.”
“Ba za mu goyi bayan wata jam’iyya da za ta sayar da ‘yancinmu ba ko kuma a yi wata yarjejeniya,” in ji kakakin ?ungiyar dattawan arewacin Najeriya Dr Hakeem Baba Ahmed.
Ya kuma ce za?en 2023 kamar jihadi ne ga ?an arewa domin ?watar kansu da ga matsaloli na rashin tsaro da talauci da rashin ayyukan yi. “Za mu yi amfani da yancinmu – muna ganin matsalolin da muke da su dole sai ?an arewa zai yi maganinsu.”
“Sai mun ga dama za mu za?i dan kudu amma ba da tsiya da zagi ba. muna iya yarda mu zabi dan kudu amma sai yan arewa sun tabbatar da zai yi shugabancin da ya fi wa?anda muke da su a yanzu,” in ji shi.

