A daidai lokacin da jam’iyyar PDP ta tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin ?an takarar shugaban kasa a jam’iyar, ita kuwa Mai dakinsa hajiya Ru?ayya Atiku Abubakar ta yaba wa shugabanin jam’iyar da kuma ‘ Ya’yan jam’iyyar baki daya da suka zabi cancanta na zaben Mai gidan ta a matsayin ?an takarar shugaban kasa.
Hajiya Ru?ayya ta bayyana hakan ne lokacin da take zantawa da manema labarai a Abuja dangane da halin da al’ummar Nijeriya ke ciki inda ta ce matu?ar alummar Nijeriya suka zabi Wazirin Adamawa a zaben 2023 za su samu saukin rayuwa a fannoni daban daban.
Da take ?arin haske dangane da kalubalan tsaro kuwa Rukayya ta ce kamar yadda ta san Maigidan ta da jajircewa akan abu tana da tabbacin zai sharewa ‘Yan Nijeriya hawaye.
Daga karshe tayi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabatar sun mallaki katin zabe domin hakan ne zai basu damar ka?a kuri’un su a lokacin zabe, kana ita kuma hukumar zabe ta taimaka ta ?ara wa’adin gudanar da aikin yi wa ‘yan kasa katin zaben.

