Site icon Muryar 'Yanci

2023: An Yi Mini Wahayin ?an Arewa Ne Shugaban ?asa – Pastor Elijah

Babban Pastor a Najeriya mai suna Pastor Elijah Ayodele ya bayyana cewa an masa wahayin abinda zai faru a shekaru mai zuwa, musanman a shekarar babbar za?e ta kasa ta 2023.

Yace a zaben 2023, ‘yan kudu su daina wahalar da kansu maganar tsayawa takarar shuyaban kasa, Saboda Dan Arewa ne zai sake zama shugaban kasa.

Yace amma za’a samu rikici wanda ba’a taba samun irinsa ba a Najeriya, yace mafita kawai shine a canjawa Najeriya fasali.

Ya baiwa Tinubu shawarar cewa kada ya wahalar da kansa tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 dan ba zai ci ba, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.

Kalaman Pastor Elijah na zuwa ne a daidai lokacin da batun zaben shekarar 2023 ke ?ara ?aukar zafi, inda sashin kudu maso yammacin Najeriya ke ganin su ya dace su karbi ragamar shugabancin kasar.

A yayin da a bangare guda yankin kudu maso gabas wato sashin Inyamurai ke han?oron ganin su samu shugabancin kasar, bisa ga la’akari da yadda aka mayar da su ‘yan baya ga dangi a mulkin Najeriya.

Exit mobile version