Kungiyar cigaban Matasan Arewa (AYCF) ta bayyana damuwa kan wasu rahotanni dake bayyana cewar wasu gungun jama’a na shirin gudanar da zanga-zanga domin haifar da rudani a bikin ranar dumukaradiyya ta 12 ga watan Yuni dake tafe.
A cikin wata takardar sanarwa da shugaban kungiyar ta matasan na Arewa Yerima Shettima ya fitar kuma aka rarraba wa manema labarai a Kaduna, ya yi tir gami da Allah wadai da duk wani shirin zanga-zanga da wasu za suyi musamman a ranar bikin 12 ga watan Yuni, wanda Najeriya ke murnar ranar Dimokuradiyya.
“Kungiyar mu ta cigaban matasa na alfahari da ranar ‘yancin dumukaradiyya ta 12 ga watan Yuni, sannan a hannu guda tana Allah wadai da duk wani shirin zanga-zanga a wannan rana.
A matsayin mu na matasa muna fata da burin ganin ha?in kai da zaman lafiya ya wanzu a tsakanin jama’a, muna da yakinin cewa tattaunawa da fahimtar juna shine mafita ga Jama’ar Najeriya ke takawa inji Shettima.
“Duk da cewa doka ta amince da aiwatar da zanga-zanga ta lumana a kasa, amma duk lokacin da ya zamana wasu na da mugun nufi sauya akalar zanga-zangar mu a matsayin ?ungiyar mu ta cigaban matasa ba ma goyon bayan wannan zanga-zangar.
Daga karshe Shugaban Kungiyar matasan ya yi kira ga dukkanin matasan Najeriya da su rungumi akidar zaman lafiya da zama jakadu nagari a cikin al’umma, sannan su kauce wa shiga dukkanin wasu al’amurra da za su iya zama barazana ga kasa.

