Site icon Muryar 'Yanci

?aukar Fansa: Sojoji Sun Hallaka Kwamandojin Boko Haram Masu Yawa

Dakarun sojojin Nijeriya sun fara daukar fansar jinin ‘yan Nijeriya akan ‘yan ta’addan Boko Haram.

Wato jama’a kamar yadda hedikwatar tsaron Nijeriya ta fitar da sanarwar cewar dakarun sojojin Nijeriya sun hallaka jagororin ‘yan Boko Haram a cikin dajin Sambisa dake kan iyakar Nijeriya da kasar Kamaru da Chadi ta jihar Borno.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa dakarun sojojin Nijeriya sun lalata sansanonin ‘yan Boko Haram tare da hallaka kwamandojin su a cikin dajin Sambisa.

Majiyar mu ta ci gaba da bayyana mana cewa tabbas dakarun Sojojin Nijeriya sun yi wa ‘ya Boko Haram babbar illa domin sun rautana kungiyar a cikin dajin Sambisa.

Muna rokon Allah Ya nuna mana karshen duk wani dan ta’addan dake rayuwa a cikin Nijeriya.

Exit mobile version