Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamnan jihar Sanata Bala Mohammed ya ce Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote ya fi fahimtar ‘yan Najeriya fiye da wasu ‘yan siyasar kasar nan, kuma babu shakka shi rahama ne a Najeriya.
Bala Mohammed ya sanar da hakan ne a Bauchi a ranar Talata yayin da jami’an gidauniyar Dangote suka ziyarcesa, a fadar gwamnatin jihar dake birnin Bauchi.
Gwamnan ya kwarzanta biloniyan dan kasuwan a kan yadda yake tallafawa mata da masu bukatar taimako a kasar nan. “Ya bayyana jarumtarsa na mutumin da yayi nasara a fannin kasuwanci inda kuma yake taimakawa ga marasa karfi da kuma duk wanda ya samu damar tallafawa,”.
“Ba wai bangaren ilimi da lafiya kawai yake ginawa ba a fadin duniya, yana gangarawa har zuwa mabukata kuma yana samarwa mutane da yawa abinci. “Daga abinda ya nuna, ya bayyana cewa ya fahimci Najeriya fiye da yawancin ‘yan siyasa saboda shi ke tallafawa masu daukar dawainiyar iyalansu.”
“Mun san yadda kamfanin Dangote yake da abubuwan da suke yi. Suna yin shi ne cikin tsari kuma a kimiyyance,” yace. Kauran bauchi ya roki Dangote ya zuba hannun jari a jiharsa Ina rokonku da ku zo ku duba abinda muke da shi a nan.
Akwai zaman lafiya a Bauchi kuma hannayen jarinku zasu samu kariya saboda yana daga cikin jihohi masu zaman lafiya a arewacin Najeriya.”

